Gwamnatin kasar Amurka tana takurawa JMI ne don ta dakatar da shirinta na makamashin nukliya saboda manufar HKI ne hakan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa Amurka tana barazana ga Iran a kan cewa idan bata amince a cimma yarjeniya da ita a kan shirinta na makamashin Nukliya ba to fa ba abinda ya rage sai zabin soje don wargwaz cibiyotyin makamashin nukliya na kasar.
Wannan bukatar ce ta HKI wacce ta yi ta nanatawa a MDD ne a kuma duk inda jami’an gwamnatinta suka yi jawabi a shekaru da dama da suka gabata. A halin yanzu Amurka na bin wannan Shirin sau da kafa. Wata majiya ta shaidawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa, a zagayen tattaunawa har 4 wadanda kasashen biyu suka gudanar za’a fahinci cewa Amurka tana bukata a wajen Amurka fiye da abunda ta gabatar a zaman taro na farko, na biyu na uku da na hudu da suka gabata.
Sai zai don tsoron kada ta kori Iran tun ba’a je ko in aba, taki ta kawo wadannan al-amura, said ai ta bayyana su a kafafen yada labarai.
Manufar tattaunawar dai kamar yadda Amurka ta bayyana itace hana Iran mallakar makaman Nukliya. Amma sai ta bayyana bas hi bane bayan zagaye na 4, manufar itace hana Iran tace makamacin Uranium kwatakwata. Abbas Argchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya manufar ta na shiga tattaunawa ba kai tsaye ba da Amurka it ace ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasa. Amma a tattaunawar da suka gabata Amurka bata ma kawo batun ba.