Amurka Tana Binciken Yadda Wasu Asiranta Na Shirin HKI Na Kaiwa Iran Hari Ya Shiga Yanar Gizo

Gwamnatin Amurka da kuma ta yahudawan Sahyoniya su na bincike don gano yadda wasu daga cikin shirye shiryensu na sirri, dangane da hare haren da

Gwamnatin Amurka da kuma ta yahudawan Sahyoniya su na bincike don gano yadda wasu daga cikin shirye shiryensu na sirri, dangane da hare haren da HKI ta shirya kaiwa Iran ya sulale ya shiga yanar gizo har duk wanda ya sou zai gan shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jaridar ‘Axion’ ta kasar Amurka ta na fadar haka. Ta kuma kara da cewa, jami’an tsaro na kasar Amurka sun damu da yadda takardun sirri na shirye shiryen da HKI take yi na  kaiwa kasar Iran hari ya sulale ya shiga shafukan yanar gizo inda kowa yake gani.

Tashar talabijin ta CNN ta bayyana cewa takardun na asiri ni wadanda ya shafi shirye shiryen HKI na maida martani kan kasar Iran,  kuma duk da cewa an rubuta ‘Top secret’ wato na sirri ne a kansu, inda banda kawayenta guda biyar kawai zasu gansu, wato suna Amurka, Australia, Canada, Newzealand da kuma Burtaniya. Sun sulale sun shiga yanar gizo.

Binciken zai fara da wadanda suke da damar ganin takardun kafin a gano wanda ko wadanda suka watsa shi a yanar gizo.

Ana saran manya manyan hukumomin leken asiri na Amurka kama daga FBI, Pentagone da kuma hukumar leken asiri na Amurka duk zasu fara bincike don gano ta inda takardun suka fita.

Wani jami’an gwamnatin Amurka ya fadawa CNN kan cewa matsalar itace mai yuwa akwai wasu takardun wadanda aka watsa amma ba’a gansu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments