Amurka Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Kai Hari Ga Ayarin Motocin Hukmar Abinci Ta Duniya A Sudan

Amurka ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kan ayarin motocin Hukumar Abinci ta Duniya a Sudan Massad Boulos, babban mai ba da

Amurka ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kan ayarin motocin Hukumar Abinci ta Duniya a Sudan

Massad Boulos, babban mai ba da shawara ga shugaban Amurka Donald Trump kan harkokin kasashen Larabawa da Afirka, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan ayarin motocin Hukumar Abinci ta Duniya a Arewacin Kordofan ta kasar Sudan a ranar Juma’a, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane.

Boulos ya jaddada cewa: Gwamnatin Trump ba ta da juriya ga abin da ya kira “kashe rayuka” da lalata tallafin da Amurka ke bayarwa.

Ya jaddada cewa lalata tallafin abinci da aka yi niyyar kai wa ga wadanda ke cikin bukata da kuma kashe ma’aikatan agaji abin kyama ne.

Tun da farko a ranar Juma’a, kungiyar likitocin Sudan ta bayar da rahoton cewa mutum daya ya mutu wasu uku kuma sun jikkata a harin, wanda wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Sudan ta danganta da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces.

A halin yanzu, Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jin Kai (OCHA) ya ruwaito cewa harin ya haifar da mutuwar mutum daya da kuma jikkata da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted