Amurka Ta yi Barazanar Kama Babban Hafsan Tsaron Venuzuwela Idan Yaki Ba da Hadin Kai

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Amurka da Donald trump ke jagoranta ta gargadi ministan cikin gidan kasar Venuzuwela Diosdado cabello da cewa shi ne mutum

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Amurka da Donald trump ke jagoranta ta gargadi ministan cikin gidan kasar Venuzuwela Diosdado cabello da cewa shi ne mutum na gaba da za ta kama idan yaki bada hadin kai ga shirin Amurka da kuma goyon bayan shugabar gwamnatin rikon kwarayar kasar domin dawo da doka da oda.

An sanar da cabello ta hanyar masu shiga tsakani cewa nuna rashin amincewa na iyar jawo a kamashi ko kuma a koreshi daga aiki kamar yadda wasu majiyoyin 3 suka bayyana cewa sojojin Amurka za su iya aiwatar da abin da suka yi wa shugaban kasar Nicolas maduro a kwanan nan akansa.

Gargadin baya bayan nan ya fito ne adaidai lokacin da kasar Amurka take kara matsin lamba kan babban jami’i a tsohuwar gwamnatin venuzuwela da ke kokarin iko da tsrin siyasar kasar bayan sace shugaban kasar Maduro da Amurka ta yi.

A ranar Asabar ce aka kama Modoru da matarsa daga gidansu dake karakas inda aka daukesu da jirgin yaki daga venuzuwela zuwa wuri mai nisan kilomita 3400 dake birnin newyork domin ya fuskanci wasu tuhume –ruhume da akai masa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted