Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya

Sahen tsaro na Pentagon na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa ya fara janye sojojinta a wasu sansanoni a kasashen Iraki da Siriya. Tashar talabijin

Sahen tsaro na Pentagon na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa ya fara janye sojojinta a wasu sansanoni a kasashen Iraki da Siriya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, bisa rahoton da sashen ya saba fitarwa a ko wani watanni 3, ya bayyana cewa Amurka da kawayenta sun kawo karshen sansanoninsu a wurare uku a fadamar kogin Furat na kasar Siriya. Kuma sun hada da ‘Green Village Mission Support Site, da ‘SansaninH2’ da kuma, da kuma  sansanin Kogin furat wanda kuma shi ne ake kira sansanin Conoco mai arzikin iskar gas.

Labarin ya kara da cewa Amurka ta wargaza gine-gine da kuma kayakin soje da wadan nan wurare, ko kuma ta bawa kungiyar kurdawa yan tawaye wacce goyon bayanta mai suna Syrian Democratic Forces (SDF).

Har yansun akwai wasu sojojin Amurka a wasu yankuna a kasashen biyu. Rahoton ya kara da cewa Amurka tana son tattara wasu sojojin a sansanin guda wasu kuma ya zamantu an rage su zuwa sojoji 1000 guda kacal.

Amurka ta shigo kasar Syriya da sunan yaki da Daesh, a lokacinda suka samu dan Desh ya zama shugaban kasar Siriya sai suna fara janyewa, wanda ya tabbatar da cewa su suka kafa Daesh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments