Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida

Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran

Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta.

Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted