Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba

A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin

A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba!

Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta.

Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.”

Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments