Jakadan Amurka na musamman a kan al-amuran gabas ta tsakiya Steve Witkoff zai tattauna da wakilai daga kasashen Masar, Qatar da Turkiya kan halin da ake ciki a gaza a yau Jumma’a a kuma birnin Miami na kasar Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa, na cewa wani jami’in gwamnati a fadar white House ya fada masa a jiya Alhamin kan cewa, batun marhala na biyu na tsagaita budewa juna wuta a Gaza ne zai mamaye tattaunawarsu.
A marhala na biyu dai, HKI zata janye daga inda take a halin yanzu a gaza, sannan za’a kafa gwamnatin Rikon kwarya wanda babu Hamas a cikinta, wacce kuma zata karbi ikon gudanar da al-amura a Gaza, sannan za’a kawo sojojin kasa da kasa masu tabbatar da zaman lafiya a yankin daga ciki har da sojojin Amurka.
Ana saran ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan Fidan ne zai wakilci kasar, sannan Mohammed bin Abdul Rahman Al-Thani na kasar Qatar Firaiministan kasar, da Badr Abdulattif ministan harkokin wajen kasar Masar zai sami halattan taron na Miami a yau injio shafin labarai na Axios.