Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba.
Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin bakin jini da Isra’ila ta yi a duniya bayan kisan kare dangi da ta yi a yankin Gaza, da ta fara tun daga watan Oktoban shekara ta 2023, wannan yasa telaviv ta bukaci abokiyarta ta ci gaba da aiwatar da aniyarta.
Ana sa bangaren jami’an gwamnatin falasdinu sun yi gargadin cewa duk wani mataki da zaa dauka na kokarin canza wani dan mamaya da wani, kwai canza sojojin isra’ila ne da na kasashen waje, idan ana iya tunawa tun a watan nuwamba ne baban jami’I a kungiyar Hamas musa abu marzuk ya bayyan cewa ba za su amince da irin wadannan matakai ba.
A baya bayan nan Washington ta mika wani daftarin kudiri ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na nemana kafa wata runduna mai suna ISF da zasu zauna a yankin gaza a kalla na tsawon shekaru biyu