Search
Close this search box.

Al’ummar Faransa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Yin Tir Da Goyon Bayan Kasarsu Ga ‘Yan Sahayoniyya  

An gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Paris na kasar Faransa don nuna adawa da goyon bayan Faransa ga Netanyahu Dubban al’ummar Faransa ne

An gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Paris na kasar Faransa don nuna adawa da goyon bayan Faransa ga Netanyahu

Dubban al’ummar Faransa ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Paris fadar mulkin kasar domin nuna kin amincewa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na nuna goyon baya ga gwamnatin Benjamin Netanyahu mai tsatsauran ra’ayi, tare da yin tir da shurun da kasashen yammacin duniya suka yi dangane da kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummar Falasdinu.

Rahotonni sun bayyana cewa: Hutun bazara a Faransa bai hana masu zanga-zangar fitowa kan titi ba. A cikin wannan zanga-zangar da ta gudana a tsakiyar birnin Paris, jama’a sun din ga rera taken cewa: Macron na da hannu wajen aikata laifukan da ake ci gaba da yi wa al’ummar Falasdinu.

Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera taken yin Allah wadai da yadda kasashen Turai ke goyon bayan Amurka da kuma matsin lamba da take yi na dora manufofin siyasa gwamnatin Benjamin Netanyahu mai tsattsauran ra’ayi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments