Aljeriya za ta kara yawan samar da man da take fitarwa a ko wace rana daga ganga 6,000 a watan Satumba, zuwa ganga miliyan 1.007 , wani mataki da kasar ba ta kai ba tsawon shekaru da dama.
Wannan ya biyo bayan matakin da Kasashe bakwai na OPEC+ suna dauka na kara ganga mai 188,000 a kowace rana, domin daidaiton kasuwar mai.
An yanke shawarar ne a lokacin wani taron bidiyo na ministocin mai na kasashen Aljeriya, Saudiyya, Iraki, Kazakhstan, Kuwait, Oman, da Rasha.
Wadannan kasashe sun amince da kara yawan ganga 188,000 a kowace rana daga watan Satumba.
Ministan man fetur na Aljeriya, Mohamed Arkab, shi ma ya halarci taron Kwamitin Kula da Haɗin Gwiwa na Ministoci (JMMC), wanda aka ɗora wa alhakin tantance bin ƙa’idodin membobin OPEC+.
Bayan taron, mahalarta sun jaddada bukatar ci gaba da yin hadin gwiwa da ci gaba da sa ido kan kasuwar mai.
Sun nanata cewa bin ka’idodin hadin gwiwa yana da mahimmanci don kiyaye daidaiton farashi a kasuwannin duniya.