Search
Close this search box.

Al-Sisi : Akwai Barazana A Yankin Saboda Yakin Isra’ila A Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya yi gargadin cewa muddin Isra’ila ta ci gaba da aikata cin zarafin da ta ke ga al’ummar Falasdinu to

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya yi gargadin cewa muddin Isra’ila ta ci gaba da aikata cin zarafin da ta ke ga al’ummar Falasdinu to za’a iya shiga cikin wami mummnan yanayi na yaki a yankin.

M. Al-Sisi ya yi wannan gargadin ne lokacin da yake ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wanda ke ziyara a yankin a kokarin cimma nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Shugaban kasar ta Masar, ya ce tilas ne dukkan bangarorin su yi taka tsantsan game da “mummunan hadarin da ke tattare da rikicin ya fadada a shiyya-shiyya, wanda zai iya haifar da bala’i.”

“Lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin da ake ci gaba da yi a Gaza, da kuma yin amfani da hikima, da kuma tabbatar da zaman lafiya’’

Al-Sisi ya ce, tilas ne tsagaita bude wuta a Gaza ya zama mafarin kasashen duniya baki daya sun amince da kafuwar kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.

Kasashen Masar, da Qatar, su ne ke gudanar da shawarwarin neman tsagaita wuta a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ta kwashe watanni 10 anayi kan al’ummar Falasdinu a Gaza.

Blinken ya tafi Masar ne daga Tel Aviv, jiya Litinin, inda ya ce Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da “shawarar ” da Amurka ta gabatar da nufin dinke barakar da ke tsakanin Isra’ila da Hamas bayan an dakatar da tattaunawar zaman lafiya a Qatar a makon da ya gabata ba tare da samun nasara ba.

Ya kuma bukaci kungiyar Hamas da ta amince da shawarar, saidai Hamas ta ce shawarwarin na tamakar daidai da bukatun Isra’ila ne.

Tuni Blinken ya isa birnin Doha, na kasar Qatar domin ingiza kokarin da ake na cimma yarjejeniyar ta tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila.

Sakataren Harkokin Wajen Amurkar ya bayyana a Qatar cewa bai kamata a bata lokaci ba game da amincewa da yarjejeniyar a yayin da yake kammala ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments