Falasdinawa akalla 26 ne suka yi shahada a yau Juma’a a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza tun bayan wayewar gari
Majiyar kiwon lafiya na Falasdinu ta sanar da cewa: Akalla mutane 26 ne suka yi shahada da suka hada da mata da kananan yara, tun bayan wayewar garin yau Juma’a sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan Zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinawa “Wafa” ya watsa rahoton cewa: Wasu Falasdinawa biyu ne suka yi shahada, yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin sojojijn mamayar Isra’ila suka kai a yankin Khirbet Al-Adas da ke arewacin Rafah, yayin da wani bafalasdine ya yi shahada sakamakon harsashin sojan mamayar Isra’ila a yankin Al-Shakoush da ke arewa maso yammacin birnin na Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Sannan wasu Falasdinawa uku sun yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai wa wata tawagar Falasdinawa hari a unguwar Sheikh Ridwan da ke yammacin birnin Gaza. Kamar yadda jiragen saman yakin sojojin mamaya suka kai hare-hare kan yankunan sansanin Jabaliya dake arewacin Zirin Gaza.
Tun da farko dai wasu Falasdinawa hudu ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani hari da jirgin saman yakin sojin mamayar Isra’ila ya kai kan wani gida na iyalan Salman da wani tanti da ke kusa da shi a yammacin yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza.