Afirka Ta Kudu Ta Dage A Kan Matsayinta Duk Tare Da Barazabar Amurka  Na Kin Halattan Taron G20

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa taron G20 a kasar

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ronald Lamola ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu na cewa

“kasarmu yentacciyar kasa ce, kan tsarin democradiya, sannan tana mutunta bil’adama, tana daidaito tsakanin kasa, babu bambamcin launin fata”

Lamola ya kara da cewa kasarsa na da tsarin zamanta kewa mai cikekken yanci daga duk wata kasa a duniya.

Ministan  ya kara da cewa, ba sauyin yanayi ne kawai muke tattaunawa a taron G20 ba,

Kafin haka sakataren harkokin wajen Amurka yace, shi ba zai halacci taro inda babu ambaton bukatun Amurka ba.

A ranakun 20-21 na watan Fabrayrun da muke ciki ne za’a gudanar da taron G20 a birnin Jorhamsboug na kasar Afirka ta kudu.

Amma Amurka tana korafin yadda Afrika ta kudu tasa HKI a gaba, kan kisan kiyashin Gaza da kuma wata dakar wacce shugaban kasar Cyril Ramaposa ya sanyawa hannu dangane da rabon filaye cikin adalci a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments