AFCON :  Mali, Morocco, Afrika ta Kudu, Masar, Najeriya, Aljeriya sun tsallake zuwa rukunin ‘yan 16

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Afrika ta Kudu ta doke Zimbabwe 3-2,

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Afrika ta Kudu ta doke Zimbabwe 3-2, yayin da Angola da Masar suka tashi canjaras 0-0 a wasansu na jiya Litini

Haka zalika a jiyan Morocco mai masaukin baki ta lallasa Zambia da 3-0 sai kuma Comoros da Mali da suka tashi ba ci 0-0.

A yau Talata idan an jima akwai karawa tsakanin Najeriya da Uganda, Haka kuma akwai fafatawa tsakanin Tanzania da Tunisia.

Akwai kuma karawa tsakanin Botswana da DR Congo.

A yayin da Benin zata fafatawa da Senegal.

Tuni dai kasashen da suka hada da Mali, Morocco, Afrika ta Kudu, Masar da kuma Najeriya da Aljeriya suka tsallake zuwa zukunin ‘yan 16.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted