Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49.
Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto.
Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan.
Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni an tsamo gawawwakin dalibai shida,ana kuma ci gaba da neman sauran.
Sauyin yanayin duniya yaa shafi kasar Afirka Ta Kudu, ta yadda a cikin shekarun bayan nan ake yawan samu ambaliyar ruwa. A watan Aprilu na 2022 an yi mamakon ruwa guguwa mai karfi wacce ta ci rayukan kusan mutane 400.