Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa,ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kaidubu 33 da 482. Sanarwar ta kuma ce, wadanda su ka jikkata ya zuwa yanzu sun kai dubu 76 da 49.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta kuma ce a cikin sa’oi 24 da su ka shude an sami shahidai 122 da kuma wadanda su ka jikkata su 156.
Sai dai har yanzu da akwai wasu daruruwan shahidai da suke a karkashin baraguzai na gine-ginen da ‘yan sahayoniyar su ka rusa gidajen da suke ciki.