Kiristoci a kasashen duniya da dama suna bukukuwan haihuwar annabi Isa (s) wanda aka haifeshi shekaru 2025 da suka gabata.
Sai dai a kasar Falasdinu inda aka haifeshi, ko kuma a garin Beitlaham a kuma cikin cocin Nativity babu wasu bukukuwan da aka saba yi , wanda kuma yake samun halattar shugwabannin Palasdinwa musamman shugaba Mahmud Abbas, Mutane garin ne kawai suke bukukuwan a garin nasu. Banda haka falasdinawa a garin da kuma sauran garuruwan Falasdinawa suna fama da matsaloli tattalin arziki masu tsanani, saboda kuntata masu wanda HKI take yi.
Sannan a sauran kasashen duniya kuma masu zanga zangar goyon bayan Falasdinawa a gaza suna ci gaba da fitowa a kan tituna a birnin Buenos Aires inda suke bukatar a kawo karshen yakin a kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take yi gaza.