Shugaban kwamitin sadarwa na Hizbullah Wafik Safa wanda ya gana da ‘yan jaridar jiya a unguwar Dhahiya dake birnin Beirut ya sanar da lokacin yin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, tare da bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu kungiyar ta Hizbullah ta kara karfi fiye da baya.
Wafik Safa ya fadawa manema labaru cewa; A yanzu kungiyar ta Hizbullah ta yi karfi sosai, kuma wannan wani lamari ne da abokan gaba su ka tabbatar da shi a filin daga.
Danagane da jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, Wafik Safa ya ce, za yi ta ne bayan gushewar cikar kwanaki 60 daga tsagaitawa wutar yaki a cikin unguwar Dhahiya dake cikin Beirut.
Har ila yau Wafik Safa ya ce, kungiyar ta Hizbullah ta shirya fuskantar kowace irin yanayi, sannan kuma ya ce, ina kwantarwa da kowa hankali cewa kar wanda ya shiga cikin damuwa.
Da yake Magana akan batun zabar shugaban kasa, Wafik Safa ya ce; Hizbullah ba za ta hau kan kujerar naki akan kowane dan takara ba, in ban da Samir Ja’a-ja’a, domin shi zai zo ne da shirin tayar da fitina.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, kungiyar ta Hizbullah a shirye take ta fuskanci kowan irin wuce gona da iri da suke ganin ta dace.
Dangane da batun yiyuwar kin ficewa sojojin Isra’ila daga wuraren da suke ciki a kudancin Lebanon bayan cikar wa’adin kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki, shugaban kwamitin sadarwar na Hizbullah ya ce, Idan hakan ta faru to Hizbullah za ta zama mai zabi na daukar matakin da ya dace.