Jagora : “Duniya Ta Amince Da Iran A Matsayin Mai Karfi A Yankin

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya karbi bakuncin shugaban kasar Massoud Pezeshkian tare da mambobin majalisar ministocinsa a yau Talata. Jagoran ya godewa shugaban kasa

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya karbi bakuncin shugaban kasar Massoud Pezeshkian tare da mambobin majalisar ministocinsa a yau Talata.

Jagoran ya godewa shugaban kasa da majalisar dokokin kasar da suka taimaka wajen kafa majalisar ministoci cikin gaggawa.

“A gwamnatocin da suka gabata, a wasu lokutan ana daukar watanni da dama kafin a kai ga kafa majalisar ministocin.

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki cewa dukkan ministocin sun samu amincewar majalisar. »

Wannan babbar nasara ce da zamu godewa Allah Ta’ala, inji jagoran.

Jagoran ya tabbatar da cewa a yanzu ya zama wajibi kowa ya taimaka da tallafawa “dukkan wadannan ministocin da suka samu amincewar shugaban kasa da majalisar dokoki” don cimma manufarsu.

Dangane da karfin siyasa kuwa, Jagoran ya yi magana game da karfin dabarun Iran:

“A cen an san Iran da kafet da man fetur kawai, Amma a yau duniya ta san Iran a ci gaban kimiyya da soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments