Najeriya: Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Fara Aiwatar Da Albashi Mafi Karanci Na Naira 70,000 Wanda Shugaban Kasa Ya Amince Da Shi

Gwamnatin jihar Adamawa a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan fara aiwatar da sabon tsarin albashi na naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi, wanda shugaban

Gwamnatin jihar Adamawa a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan fara aiwatar da sabon tsarin albashi na naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanyawa hannu a cikin yan makonnin da suka gabata.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin Ahmadu Fintiri ta amince ta fara biyan sabon tsarin albashi wanda mafi karancinsa naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar, daga karshen watan Augusta da muke ciki, sannan kananan hukumomin jihar kuma daga cikin watan Satumba mai kamawa.

Labarin ya kara da cewa sauran gwamnonin jihohin kasar dai sun bayyana cewa ba zasu iya biyan sabon tsarin albashin ba saboda matsalolin tattalin arzikin da suke fama dasu.

Wannan sanarwan dai ya sa ma’aikata da dama a jihar suka nuna farin cikinsu da kuma godiya ga gwamnan Fintiri.

Daily Trust ta bayyana cewa, wasu da dama wadanda suka karbi albashinsu na wannan watan sun tabbatar da cewa an karamasu al-bashi bisa sabon tsarin kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments