Kwamandan Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Ya Amince Da Zaman Sulhun Kasar

Kwamandan dakarun kai daukin gaggawa ya bayyana matsayinsa na shiga cikin tattaunawar kasar Switzerland don kawo karshen yaki a Sudan Kwamandan Rundunar kai daukin gaggawa

Kwamandan dakarun kai daukin gaggawa ya bayyana matsayinsa na shiga cikin tattaunawar kasar Switzerland don kawo karshen yaki a Sudan

Kwamandan Rundunar kai daukin gaggawa ta Rapid Support Forces ta Sudan, Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), ya jaddada amincewarsa da gayyatar da Amurka ta yi masa na shiga cikin tattaunawar birnin Geneva na kasar Switzerland wanda aka shirya yi a cikin wannan wata na Agusta.

A wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar litinin, Hemedti ya yi kira ga sojojin Sudan da su amsa kiran zaman lafiya domin rage radadin al’ummar Sudan. Hemedti ya yi iƙirarin cewa: Suna gabatar da wannan kira da dukkan ƙarfin hali, duk da nasarar da suke samu a fagen yakin kasar.

Kwamandan kungiyar ta Rapid Support Forces ya yi furuci da cewa: Kasar Sudan ta kama hanyar rugujewa sakamakon yakin da ya haifar da hargitsi da kuma rashin tsaro mai yawa, yana mai jaddada cewa: Irin wannan lamarin a kodayaushe yana tare da yaƙe-yaƙe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments