‘Yan Gwagwarmaya Sun Kashe Wani Tsageran Bayahuden Sahayoniyya A Falasdinu

An kashe wani bayahuden sahayoniyya tare da raunata wani na daban a wani hari da a kai a kwarin Jordan da ke yammacin gabar kogin

An kashe wani bayahuden sahayoniyya tare da raunata wani na daban a wani hari da a kai a kwarin Jordan da ke yammacin gabar kogin Jordan

Rahotonni sun bayyana cewa: Wani tsageran bayahuden sahayoniyya ya halaka, yayin da wani na daban ya samu raunuka, sakamakon harbin da aka yi kan motarsu ​​a yankin gabar yamma da kogin Jordan, kuma maharin ya samu nasarar tserewa daga wurin.

Shafin watsa labarai na yahudawan sahayoniya “Doron Kadosh” ya bayyana cewa: Motar da take dauke da maharani da suka yi harbin ta tsere daga wurin, kuma sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da farautar su.

A gefe guda kuma, majiyar dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta dauki alhakin kai harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments