Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan Mumtaz Zahra ta musanta zargin jaridar ‘Jeruselempost’ ta HKI wacce ta bayyana cewa akwai yarjeniyar tsaro ta sirri tsakanin Pakistan da Iran a duk lokacinda zata kaiwa HKI hare hare.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zahra tana fadar haka a jawabin da ta saba yi wa yan jaridu na mako-mako.
Zahra ta kara da cewa gwamnatin HKI tana son rikita harkokin zamantakewa a kasar Pakistan da yada irin wadan nan karyayyaki.
Jaridar Jeruselem Post dai ta ce kasar Pakistan ta yi alkawarin bawa kasar Iran makamai masu linzami, masu cin matsakaicin zango a duk lokacinda yaki ya barke tsakaninta da HKI.
Kasar Pakistan dai ta halarci taron kungiyar kasashen musulmi ta IOC wanda Iran ta kira a birnin Jidda na kasar Saudiya inda suka tattauna batun kissan shugaban kungiyar Hamas a Tehran a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata, da kuma ci gaba da kissan kiyashin da sojojin HKI suke wa Falasdinawa a Gaza.
Iran dai ta sha alwashin daukar fansa jinin Haniyya a kan HKI.