HKI Ta Kama Limamin Masallacin Al-Aksa Saboda Ya Yi Addu’a Wa Shahid Isma’ila Haniya

Yan sanda a HKI sun kama limamin masallacin Al-Aksa Sheikh Ekrima Sabri bayan ya yi addu’a wa Shahid Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamasa a lokacinda

Yan sanda a HKI sun kama limamin masallacin Al-Aksa Sheikh Ekrima Sabri bayan ya yi addu’a wa Shahid Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamasa a lokacinda yake bada sallar Jumma’a.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa sheikh Sabri a cikin khudubarsa ta sallar Jumma’a a masallacin Al-Aksa a jiya, ya yi addu’a wa shahid Isma’il Haniyya ya kuma roko All..T ya jikansa.

Wasu jaridun HKI sun bayyana cewa yansandan HK sun tafi da sheikhin malamin zuwa ofishinsu a birnin Qudus inda suka fara yi masa bincike don tabbatar da cewa maganganunsa dangane da shahadar Haniya, da kuma addu’ar da ya yi na nema masa gafara ya ci karo da manufofin gwamnatin HKI.

Wasu kafafen yada labaran yahudawan sun bayyana cewa yansanda yahudawan sun je gidan Sheikh Ekrama Sabri da ke unguwar al-Sawana na birnin Al-Quds ne, a jiya da yamma sun kuma tafida shi, don bincike.

Jaridar Jeruselem Post ta bayyana cewa mai yuwa gwamnatin HKI ta soke takardunsa na zama a cikin Falasdinu da aka mamaye, Idan har ya tabbata ya yi wa Isma’ila Haniyya addu’a.

Wasu kafafen yada labaran yahudawan sun bayyana cewa an kama Sheikh Sabri ne tare da umurnin ministan harkokin cikin gida na HKI, Itamar Ben-Gvir.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments