Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabatar da ta’aziyyarsa ga dan shahidi Isma’il Haniyah
A safiyar jiya Alhamis ne, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar jana’izar Sheikh Isma’il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Falasdinu wanda yahudawan sahayoniyya suka aiwatar da kisan gilla kansa da mai tsaronsa a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Laraba.
Bayan kammala sallar jana’izar dan shahidi Isma’il Haniyah ya bayyana a gaban Jagoran juyin juya halin Musulunci, inda Jagoran ya rungume shi, ya yi masa jaje tare da jaddada alhininsa ga rashin babban mujahidin da ya gudanar da rayuwarsa mai albarka a fagen gudanar da hidima ga addinin Musulunci da dan Adamtaka, ya kuma nemi ya isar da sakon ta’aziyarsa ga dukkan ‘yan uwansa da dangin shahidin madaukaka.