Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya zanta ta wayar tarho tare da tokwaransa na kasar Turkiya Hakan Fidan dangane da shahadin shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniya a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministocin sun yi allawadi da HKI saboda kissan shugaban kungiyar ta Hamas, sun kuma kara da cewa wannan halin na ta’adancin da HKI take aikatawa ba ya nufin zaman lafiya a yankin.
Mukaddashin ministan harkokin wajen JMI ya godewa kasar Turkiyya kan halattar bukin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan, ya kuma yi fatan dangantaka tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da kara karfi.
A nashi bangaren Hakan Fida ya gabatar da taziyyarsa ga kasar Iran da kuma sauran musulmi dangane da shahadar Isma’ila Haniyya, sannan yayi allawadi da ayyukan ta’addancin HKI na kashe Haniyya da kuma falasdinawa a gaza da sauran yankunan kasar falasdinu da ta mamaye.
Yace kasar Turkiyya na goyon bayan JMI kan duk matakin da ta dauka saboda keta huruminta da HKI tayi, tana kuma goyon bayan duk abinda al-ummar musulmi suka tsaya a kai dangane da kissan shugaban Hamasa Isma’il Haniyya.