An Sake Bude Tashar Jiragen Sama Na Bozal-Muluz Na Kasar Faransa Bayan Da Aka Rufe Shi Saboda Barazanar Tashin Bom

Gwamnatin kasar Faransa ta bada sanarwan sake bude tashar jiragen sama na birnin Bozal-Muluz, wanda ke kan iyakar kasar da kasar Sweden da kuma Jamus,

Gwamnatin kasar Faransa ta bada sanarwan sake bude tashar jiragen sama na birnin Bozal-Muluz, wanda ke kan iyakar kasar da kasar Sweden da kuma Jamus, bayan da aka bada sanarwan rufe ta saboda barazanar tashin bom.

Kamfanin dillancin labaran  IRNA na kasar Iran ya ce: a yau Jumma’a 26 ga watan Yuli ne ake bukukuwan bude gasar Olympic na wannan shekara ta 2024 a birnin Paris na kasar ta Faransa, don haka tashoshin jiragen saman kasar duk sune cike da matafiya wadanda suke son halattar bukukuwan.

A halin yanzu zai an sami jinkiri na tashin wasu jiragen saman, amma da dama zasu tashi kamar yadda aka tsara bayan an sake bude tashar.

Har’ila yau wasu labaran sun bayyana cewa jiragen kasa masu sauri na kasar ta faransa sun sami matsala a harkokin zarga zirga a kasar saboda zagon kasa da aka yiwa kamfanin, don haka hukumar jiragen kasa ta kasar ta bada sanarwan cewa ba zata iya komawa aiki ba sai nan mako guda a lokacinda ake saran za’a kammala gyare gyare –gayren matsalolin da aka samu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments