Iran Tana Shirin Harba Taurarin Dan’adam 4 A Shekarar Bana

Hukumar da take kula da ilimin sararin samaniya ta Iran ta sanar da cewa a cikin wannan shekarar ta hijira shamshiyya 1403, yana mai cewa

Hukumar da take kula da ilimin sararin samaniya ta Iran ta sanar da cewa a cikin wannan shekarar ta hijira shamshiyya 1403, yana mai cewa taurarin dan’adam din da za a harba za su kasance a tsakanin 6 zuwa 8 a jumlace.

A yau Laraba ne dai shugaban hukumar sararin samaniyar na Iran Hassan Salariyeh ya gabatar da taron mamena labaru da a ciki ya yi bayanin yadda ayyukan nasu a wannan shekarar za su kasance..

Har ila yau, ya ambaci yadda tuni aka riga aka harba taurarin dan’adam na “Kauthar”, “Zafar2” da “Tulu’ 3.

Bugu da kari wani sashe na bayanin nashi, Salariyeh ya yi bayani akan yadda ake samun cigaba a fagen bunkasar ilimin sararin samaniya da kuma gano sabbin abububuwa.

Daga cikin cigaban da Iran din ta samu da akwai kera rokokin da ake harba taurarin dan’adam da su, masu cin nisan kilo mita 1500 da kuma kera kwatankwacin hasken wata.

Hassan Salariyeh ya kuma ce; A nan gaba, matukar wata kasa ba ta da masaniya akan ilimin sararin samaniya, to kuwa za ta fuskanci matsaloli a fagagen tattalin arziki da tafiyar da harkokin yau da kullum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments