Basshar Asad:   Yin Gwgawarmaya Da “Yan Sahayoniya Wajibi Ne

Shugaban Kasar Syria, Dr. Basshar Asad, ya bayyana cewa, yin gwgawarmaya da fuskantar abokan gaba ‘yan sahayoniya wani abu ne wanda ya zama wajibi. Shugaban

Shugaban Kasar Syria, Dr. Basshar Asad, ya bayyana cewa, yin gwgawarmaya da fuskantar abokan gaba ‘yan sahayoniya wani abu ne wanda ya zama wajibi.

Shugaban na kasar Syria ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da kungiyar Injiniyoyi larabawa a jiya Litinin, inda ya kara da cewa; Yin riko da manufofi shi ne ginshiki na tushe na yin gwagwarmaya a tsakanin al’ummar Falasdinu.

Shugaban kasar na Syria ya kuma kara da cewa; Duk da irin wahalhalu da yanayi maras dadi da al’ummar Falasdinawa suke ciki, amma a lokaci daya hakan ya kara wa Falasdinawa karfi da imani.

Tun da fari, ma’aikatar harkokin wajen Syria ta fitar da wani bayani da a ciki ta yi ishara da wuce gona da irin da ‘yan sahayoniya suke yi akan kasar Syria ta hanyar kai mata hari, tare da yin suka akan yadda kungiyoyin kasa da kasa akan wannan keta dokokin na duniya da ‘yan sahayoniya suke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments