Iran Ta Jinjinawa Tsayin Damar Al’ummar Kasar Yemen Wajen Fuskantar HKI

Babban jami’in diplomasiyyar Iran   Ali Bakiri Kani, wanda ya gana ta wayar tarho da Muhammad Abdussalam na kasar Yemen, ya yi tir da harin da

Babban jami’in diplomasiyyar Iran   Ali Bakiri Kani, wanda ya gana ta wayar tarho da Muhammad Abdussalam na kasar Yemen, ya yi tir da harin da HKI ta kai wa kasar Yemen, tare da kara da cewa, Iran tana goyon bayan Yemen da gwagwarmayar da take yi wajen fuskantar HKI.

Bugu da kari, Ali Bakiri Kani, ya bayyana abinda mutanen Yemen din suke yi da cewa abin alfahari ne ga dukkanin al’ummar musulmi.

Bugu da kari bangarorin biyu sun  tattauna dangane da halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

A nashi gefen, Muhammad Abdussalam wanda shi ne kakakin gwamnatin kasar Yemen, ya yaba wa jamhuriyar musulunci ta Iran,saboda yadda take goyon bayan al’ummar Yemen da kuma gwgawarmayarsu akan HKI.

Kakakin gwamnatin ceton kasar ta Yemen, ya kuma bayyana batun Falasdinu da cewa, wani abu ne da ya shafi dukkanin al’ummar musulmi, tare da jinjinawa Iran akan yadda take tsayin daga wajen bayar da kariya ta dukkanin bangarori ga masu fada da ‘yan sahayoniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments