Gwamnatin mulkin soji ta kasar Sudan, ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar na maraba da sabon jakadan Iran a kasar Hassan Shah Hosseini, a gabar da huldar kasashen biyu ke shiga wani sabon mataki.
Shugaban kwamitin ikon mulkin Sudan, kana shugaban rundunar sojin kasar, Abdel Fattah al-Burhan ya karbi takardar nadin sabon jakada na Iran dake kasar a birnin Port Sudan dake gabashin kasar, sannan shugaba Burhan ya yi ban kwana da Abdulaziz Hassan Saleh, sabon jakadan kasar Sudan da zai yi aiki a Iran.
A shekarar 2016, Saudiyya ta yanke huldarta da Iran, kana Sudan da wasu karin kasashen suka bi sahunta.
Amma a ran 9 ga watan Oktoban shekarar 2023, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fitar da wata sanarwa cewa, an koma huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sudan da Iran.