Yahudawan Yan Share Wuriu Zauna Sun Yi Wa Yayan Wata Kungiyar Bada Agaji Duka A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Yahudawan sahyoniyya yan share a yankin yamma da kogin sun farwa wasu yan kasashen waje masu sa kai wadanda suke taimakawa Falasdinawa a gonakinsu a

Yahudawan sahyoniyya yan share a yankin yamma da kogin sun farwa wasu yan kasashen waje masu sa kai wadanda suke taimakawa Falasdinawa a gonakinsu a yankin yamma da Kogin Jordan inda suka yi masu dukan kawo wuka saboda taimnakon Falasdinawa a ayyukan noma da suke yi.

Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa yan kasashen wajen mutum 8 ne mafi yawansu Amurkawa.

David Hummel daya daga cikin yan kasashen wajen mai ‘yan kasancin’ na Amurka da Jamus ya bayyana cewa, yahudawan sun yi masu duka da sanduna da kuma karafa, don hanasu taimakawa Falasdinawa a kyautata ayyukan noma.

Wasu daga cikinsu dai suna jinya a wasu asbitoci a yankin, yamma da kogin Jorda. Har’ila yau wasu majiyoyin falasdinawa sun bayyana cewa akwai wasu falasdinawa tare da su da aka jiwa rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments