Rundunar Sojin Yeman ta kaddamar da sabbin hare-hare masu girgizawa kan Isra’ila da Amurka

Dakarun Yaman sun kai farmaki guda biyu, daya ya nufi  wani birnin da Isra’ila ta mamaye, daya kuma a kan wani jirgin ruwan Amurka a

Dakarun Yaman sun kai farmaki guda biyu, daya ya nufi  wani birnin da Isra’ila ta mamaye, daya kuma a kan wani jirgin ruwan Amurka a tekun Bahar Maliya.

Dakarun na Yemen sun kai wani samame na sojan sama a kan muhimman wurare a Umm al-Rashrash [Eilat] da makamai masu linzami da dama, tare da cimma burin da aka ayyana cikin nasara, in ji kakakin rundunar sojojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree a ranar yau Lahadi.

Bayanin nasa da aka watsa ta gidan talbijin ya zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ta kai farmaki kan tashar jiragen ruwa ta Hodeidah a yemen da tashar wutar lantarki a birnin, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da kuma tashin gobara.

Saree ya yi karin bayani da cewa, rundunar ta YAF ta kuma kai hari kan jirgin ruwan Amurka “Pumba” a cikin tekun Bahar Maliya da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda suka samu jirgin ruwan kai tsaye.

Kakakin YAF ya tabbatar da cikakken ‘yancin kare kasar daga hare-haren Amurka da Birtaniya, da kuma shishigi na sra’ila.

Bugu da kari, Saree ya sha alwashin mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Yemen, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane 90, inda marrtanin nasu zai kasance mai zafi matuka.

Birgediya Janar Saree ya kammala da bayyana kwarin gwiwa da cewa, “Ayyukan da sojojin Yaman suke yi a yankin da aka ware a baya na aikin sojan ruwa a kan jiragen ruwa na Isra’ila, Amurka, da Burtaniya, ko kuma wadanda ke zuwa tashar jiragen ruwa a Falasdinu da ta mamaye, ko mu’amala da haramtacciyar kasar Isra’ila, za su ci gaba har sai am daina kai hare-haren kisan kare dangi kan al’ummar Gaza.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments