Katsewar Intanet Ya Shafi Manyan Kamfanonin A Duniya

Katsewar intanet ta haifar da tsaiko ga manyan kamfanoni a duniya da sanyin safiyar Juma’a. Masu amfani da fasahar Microsoft a fadin duniya, ciki har

Katsewar intanet ta haifar da tsaiko ga manyan kamfanoni a duniya da sanyin safiyar Juma’a.

Masu amfani da fasahar Microsoft a fadin duniya, ciki har da bankuna da kamfanonin jiragen sama, sun ba da rahoton cewa an samu katsewar intanet a ranar Juma’a, sa’o’i kadan bayan da kamfanin ya sanar da cewa ana kan shawo kan matsalar da ta danganci rashin samun damar amfani da manhajar Microsoft 365 da sauransu.

Babu cikakken bayani game da takamaimai abin da ya jawo katsewar ta intanet. Sai dai Microsoft ya wallafa wani sako a shafin X da ke cewa an soma shawo kan matsalar ko da yake mutane a faɗin duniya suna ci gaba da bayyana kalubalen da suke fuskanta na katsewar intanet.

Shafin intanet na DownDetector, wanda ke bin diddigin yadda ake amfani da intanet, ya ce an samu katsewar intanet a kamfanonin bayar da biza, da kamfanin samar da tsaro na ADT da Amazon, da kuma kamfanonin jiragen sama ciki har da American Airlines da Delta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments