Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Badruddeen Huthi ya bayyana cewa jawan jiragen ruwan da sojojin ruwa na Yemen suka kaiwa farmaka a tekun maliya ko (red Sea) ya zuwa yanzu sun kai jirage 170.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a jawabin mako makon da ya saba gabatarwa a ranakun Alhami. Ya kuma kara da cewa jiragen da abin ya shafa kuma sun hada da na Amurka, Burtaniya da kuma na HKI wadanda suke nufin haramtacciyar kasar.
Ya kuma kara da cewa a wannan makon kadai sojojin Yemen sun kai hare hare har 25 kan jiragen, a tekun Maliya tare da amfani da makamai masu linzami samfurin ballistic da jiragen yaki masu kunan bakin wake da kuma kwale kwale masu sauri.
Huthi ya kara da cewa hare haren sojojin Yemen sun gurgurta tattalin arziki HKI musamman na kudaden shigowar da take samu ta tashar jiragen ruwa na Ummu Rashrash ko (Ilat) da ke gabar tekun Akaba.
Ya kuma kara da cewa abinda yake faruwa a HKI a halin yanzu, shi ne hali mafi muni wanda gwamnatin HKI ta taba shiga tun bayan kafuwarta shekaru 76 da suka gabata wato a shekara 1948.
Ya ce tun lokacin fara yaki a Gaza ya zuwa yanzu HKI ta rufe kamfanoni 46,000 sanadiyyar hare haren dakaru masu gwagwarmaya daga kasar Yemen, Lebanon da kuma kasar Iraki.