Mohammed Hamid Jabara wani kwamandan dakarun kungiyar Hamas a kasar Lebanon ya yi shahadi bayan da makami mai linzami wanda wani jirgin yakin HKI ya fada kan motarsa a garin Ghazz na yankin Bekaa a kasar Lebanon a jiya Alhamis da yamma.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai na kasar Lebanon na fadar cewa Jabara ya kasance shugaban kungiyar Falasdinawa taAl-Jamaa al-Islamiya a kasar Lebanon sannan mayakan kungiyar suna yaki kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tun cikin watan Octoban shekarar da ta gabata.
Bassam Hamoud mataimakin shugaban kungiyar ya bayyana cewa kissan shugaban kungiyar Jabara wanda makaman linzami na HKI yayi a garin Ghazz na yankin Bekaa na kasar Lebanon ba zai hana yayan kungiyar ci gaba da gwagwaramaya da HKI ba.
Kafin haka dai HKI ta sha kashe shuwagabannin kungiyoyin Falasdina masu gwagwarmaya da ita a kasar Lebanon . Daga cikinsu akwai Mohamed Naim Nasser da kuma Taleb Abdullah da sauransu.