Abdumalik Husy Ya Zargi Amurka Da Yin Tarayya A Kashe Mutanen Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Abdulmalik Badruddin al-Husy ya zargi da cewa ta yi tarayya da HKI a laifukan da take tafkawa a Gaza.

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Abdulmalik Badruddin al-Husy ya zargi da cewa ta yi tarayya da HKI a laifukan da take tafkawa a Gaza.

Shugaban kungiyar ta Ansarullah wanda ya gabatar da jawabi ya kuma ce; HKI ce ke wakiltar duniyar kafrici saboda harin da ta kai wa Gaza, kuma yahudawa ‘yan sahayoniya su ne ke dauke da tutar dagudanci a wannan zamanin.

Har ila yau Abdulmalik ya zargi wasu kasashen larabawa da cewa; suna bayyana kawukansu a matsayin lemar larabawa,amma kuma a lokaci daya suna taimakawa abokan gaba ta hanyar aike musu da kayan masarufi.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda aka sami karuwar bunkasar alaka a tsakanin wasu kasashen larabawa da kuma ‘yan sahayoniya a wannan lokacin,akan abinda yake faruwa a Falasdinu kuwa sun zama ‘yan kallo.

Dangane da halin karancin abinda da ake fama da shi a yankin, Abdulmalik al-Husy ya ce; Babu wata al’umma a duniyar nan da take fama da karancin abinci kamar ta  Gaza.

Har ila yau ya nuna cewa yanzu a duniya babu wani yanayi da ya fi ban mamaki kamar yadda musulmi da larabawa su ka zama ‘yan kallo akan abinda yake faruwa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments