Jagoran Juyi Zan Gana Da ‘Yan Majalisa A Ranar Lahadi Mai Zuwa

A ranar 21 ga watan Yulin nan da ake ciki, jagoran juyin juya halin musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamnei zai gana da ‘yan majalisar  shawarar

A ranar 21 ga watan Yulin nan da ake ciki, jagoran juyin juya halin musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamnei zai gana da ‘yan majalisar  shawarar musulunci ta Iran,kamar yadda wani dan majalisa ya ambata.

Wannan ganawar dai za a yi ta ne bayan da aka  kaddamar da sabuwar Majalisar a ranar 28 ga watan Mayu 2024. A yayin bikin kaddamar da sabuwar majalisar an sami halartar manyan jami’an gwamnati da su ka hada da mukaddashin shugaban kasa Muhammad Mukhbari, babban mai shari’a na kasa ghulam Husain Muhseni Ejeh,sai kuma manyan kwamandojin soja.

A yayin wannan zaman an zabi Muhammad Bakir Ghalibaf a matsayin sabon shugaban Majalisar na tsawon shekara daya.

Ganawar da ‘yan majalisar za su yi da jagoran juyin musulunci zai kara karfafa rawar da Majalisar take takawa ne a cikin harkokin yau da kullum na rayuwar al’ummar kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments