‘Yan sandan London sun kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da dama

Jami’an tsaron gwamnatin Burtaniya sun kama mutane da dama da suke jerin gwanon nuna goyon baya ga al’ummar falastinu, da kuma yin kira da a

Jami’an tsaron gwamnatin Burtaniya sun kama mutane da dama da suke jerin gwanon nuna goyon baya ga al’ummar falastinu, da kuma yin kira da a akawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila take aikatawa a Gaza.

Wakilin Al Mayadeen a Landan ya ruwaito cewa, ‘yan sandan Birtaniya sun kewaye wasu gungun matasa da suka fito kan tituna domin nuna goyon bayansu ga Gaza, inda suka hana su gudanar da zanga-zanga tare da daga tutar Falasdinu.

Rahoton ya kara da cewa, ‘yan sandan sun hana matasan zuwa majalisar dokokin Birtaniya a birnin Landan, hakan na kuma  sun kama wasu magoya bayan Falasdinu  da dama a lokacin da Sarki Charles ke gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin kasar, inda ya bayyana shirin Sir Keir Starmer ga Birtaniya.

Rahoton ya kara da cewa, a lokacin da aka tambayi daya daga cikin masu zanga-zangar a lokacin da ‘yan sanda suka kama ta, ko  mene ne sakonta ga al’ummar Palastinu, sai ta amsa da cewa, “Ku ‘yantar da Falasdinu ku ‘yantar da al’ummar Gaza da ke fuskantar kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments