Rwanda: Kagame ya sake lashe zaben shugaban kasa karo na 4

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya shirya wa kansa wa’adin shugabanci na hudu a ranar Talata bayan da ya samu kashi 99.15 cikin 100 na

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya shirya wa kansa wa’adin shugabanci na hudu a ranar Talata bayan da ya samu kashi 99.15 cikin 100 na sakamakon zaben da ke fuskantar ‘yan adawa biyu.

A wani jawabi daga hedkwatar jam’iyyarsa ta Rwandan Patriotic Front (RPF), Kagame mai shekaru 66 da haihuwa, ya godewa ‘yan kasar ta Rwanda da suka kara masa karin shekaru biyar a kan karagar mulki.

“Sakamakon da aka gabatar ya nuna cewa an samu maki sosai, wadannan ba alkaluma ba ne kawai, ko da kashi 100 bisa 100 ne, wadannan ba adadi ba ne kawai,” Kagame ya fadawa magoya bayansa a wani jawabi a hedkwatar  jam’iyyar Rwandan Patriotic Front (RPF).

Ya kara da cewa “Wadannan alkaluma sun nuna amana, kuma shi ne abin da ya fi muhimmanci.”

“Ina fatan tare zamu iya magance dukkan matsalolin.”

Ana sa ran kammala sakamakon wucin gadi nan da ranar 20 ga Yuli, inda ake saran sakamako na karshe a ranar 27 ga Yuli.

“Gabaɗaya, tsarin gudanar da zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ,” in ji Hukumar Zaɓen ƙasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments