Iran Ta Yi Allawadai Da Hare Haren HKI Kan Makarantar UNRWA A Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya yi allawadai da hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wata makarantar hukumar bada

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya yi allawadai da hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wata makarantar hukumar bada agaji ta MDD a Palasdinawa UNRWA atakaice.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ta nakalto Ka’ani yana fadar haka a shafinsa na X a jiya da yamma, ya kuma kara da cewa ta’asan da sojojin HKI suke aikatawa a Gaza su ne zasu zama sanadiyyar rushewarta nan gaba.

A jiya Lahadi ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan wata makarantar UNRWA a gaza inda mutane 12 suka kai ga shahada a yayinda wasu kimani 70 suka ji rauni. Sannan akwai yiyuwar karuwar yawan wadanda suka rayukansu sanadiyyar munin raunukan da wasu daga cikinsu suka ji a wadannan hare hare.

Daga karshen Kan’ani ya kammala da cewa kasashen yamma sun yi shiru da bakunansu dangane da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza, don haka suna da hannu a cikin kisan kiyashin da HKI take yi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments