Jami’an Tsaron Rasha Sun Kama Dan Leken Asirin Ukraine Da Ya Yi Yunkurin Kashe Jami’an Rasha

Jami’an tsaron Rasha sun kama wani dan leken asiri da ya shirya kashe manyan shugabannin ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha Hukumar tsaron tarayyar Rasha ta

Jami’an tsaron Rasha sun kama wani dan leken asiri da ya shirya kashe manyan shugabannin ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha

Hukumar tsaron tarayyar Rasha ta wallafa wani faifan bidiyo na kama wani jami’in da a karkashin jagorancin hukumar leken asirin kasar Ukraine ya shirya kashe wasu manyan jami’an ma’aikatar tsaron kasar Rasha guda uku a birnin Moscow fadar mulkin kasar, kuma jami’an tsaron kasar ta Rasha sun samu nasarar lalata abubuwa masu fashewa da ke hannun dan leken asirin.

Jami’an tsaron Tarayyar Rasha sun yi nuni da cewa wanda ake tsare da shi na gab da aika wasiku da suke cike da bama-bamai a matsayin nau’in kyautuka ga adireshin jami’an da aka yi niyya halaka su.

Abin lura shi ne cewa wanda aka kama dan kasar Rasha ne, kuma an haife shi ne a shekara ta 1994.

Jami’an tsaron Rasha sun wallafa wani hoton bidiyo na lokacin da aka kama mutumin da ke shirin kashe jami’an na Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments