Shugaban Iran Ya Jinjinawa ‘Yan Gwagwarmaya Kan Taka Burki Ga ‘Yan Sahayoniyya

Sabon shugaban kasar Iran ya amsa sakon taya murna da Sayyid Nasrallah ya aiko masa tare da jaddada ci gaba da ba da goyon baya

Sabon shugaban kasar Iran ya amsa sakon taya murna da Sayyid Nasrallah ya aiko masa tare da jaddada ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yan gwagwarmaya da dukkan karfinsa

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a cikin wasikar da ya rubuta ga babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah ya jaddada cewa: A ko da yaushe Iran tana goyon bayan juriya da al’ummar yankin suke yi da mayar da martani kan haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya.

Zababben shugaban na Iran ya kara da cewa: Goyon bayan gwagwarmayar ya samo asali ne daga manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeini (Allah Ya kara masa yarda) da kuma umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khameine’i, kuma Iran zata ci gaba da mara baya ga gwagwarmaya da dukkanin karfinta.

Ya ci gaba da cewa: Yana da tabbacin cewa goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya a yankin ba zai bar wannan haramtacciyar kasa ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na tada fitina da ta’addanci ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da sauran al’ummomin yankin ba.

Shugaba Bazashkian ya karkare da cewa: Yana godiya da neman addu’o’i, kuma yana rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kara daukaka da kima ga Nasrullahi, da wadata da ci gaba ga al’ummar kasar Labanon, da taimakon Ubangiji ga jaruman gwagwarmayar Musulunci masu sadaukar da kansu saboda kare kimar dan Adamtaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments