Za A Yi Muhawara A Tsakanin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Da Su Ka Rage A Gobe Litinin

Bayan da zamana ‘yan takara biyu ne kadai su ka rage a zaben shugaban kasa da za a yi zagaye na biyu, a gobe Litinin

Bayan da zamana ‘yan takara biyu ne kadai su ka rage a zaben shugaban kasa da za a yi zagaye na biyu, a gobe Litinin da za bude tattaunawa a tsakaninsu ta kafafen watsa labarun kasa.

A gebe Litinin din ‘yan takarar biyu; Sa’id Jalili da Fizishkiyan za su yi muhawarar ne akan manufofinsu wanda kafafen watsa labarun kasa za su watsa kai tsaye. Bugu da kari, za a yi zagae na biyu na muhawarar ne a ranar Talata wanda shi ma zai kasance da misalin karfe; 9;30 na marece.

 Kakakin hukumar zabe ta Iran ne Muhsin Islami ya sanar da sakamakon zabe a jiya Asabar dake nuni da cewa za a je zagaye na biyu a tsakanin Sa’id Jalili da kuma  Mas’ud Fizishkiyan.

Shi dai Ma’ud Fizishkiyan ya sami kuri’u miliyan 10 da dubu dari hudu da goma sha biyar da dari daya da cas’is da daya, yayin da Sa’id Jalili bai binsa ya sami kuriu miliyan 9 da dubu dari 473 da 298. Sai dai babu wanda ya iya samun kason da ake da bukatuwa da shi, domin kai wa ga nasara.

A ranar juma’a mai zuwa ne za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a tsakanin mutanen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments