Kasar Rasha Ta Jaddada Ci Gaba Da Gudanar Da Yarjejeniya Da Ta Kulla Da Kasar Iran

Gwamnatin Rasha ta jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da aiki kan manyan yarjeniyoyin da ta kulla da kasar Iran Gwamnatin Rasha ta ce

Gwamnatin Rasha ta jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da aiki kan manyan yarjeniyoyin da ta kulla da kasar Iran

Gwamnatin Rasha ta ce tana ci gaba da aiki kan muhimmiyar yarjejeniya ta hadin gwiwa da Iran, inda hakan yake matsayin alama ta kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta shaidawa manema labarai a birnin Moscow a yau Laraba cewa: Yanzu haka suna aiki kan yarjejeniyar da suka kulla da kasar Iran kuma watakila labarin ya yadu, kuma yanzu haka ana kan aiki kan babbar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Rasha.

Bayanin nata ya yi nuni da wata cikakkiyar yarjejeniya ta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da aka shafe tsawon shekaru ana tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Tun a watan Janairu ne, Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce an kammala sabuwar yarjejeniya tsakanin kasashen biyu da ke nuna haɓakar ci gaba da ba a taba gani ba a dangantakar Rasha da Iran.

Kamar yadda a cikin shekaru biyu da suka gabata, kasashen biyu sun karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments