Kasar Rasha Ta Jaddada Ci Gaba Da Gudanar Da Yarjejeniya Da Ta Kulla Da Kasar Iran

Gwamnatin Rasha ta jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da aiki kan manyan yarjeniyoyin da ta kulla da kasar Iran Gwamnatin Rasha ta ce tana ci gaba da aiki kan muhimmiyar yarjejeniya ta hadin gwiwa da Iran, inda hakan yake matsayin alama ta kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen […]

Tsohon Fira Ministan Yahudawa Ya Ce: H.Kasar Isra’ila Tana Cikin Halin Tsaka Mai Wuya

Tsohon fira ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana cikin hali mafi muni da wahala tun shekara ta 1948, sakamakon ƙaurace mata da duniya ta yi Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Naftali Bennett ya yi kira ga yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da kada su bar haramtacciyar kasar Isra’ila da […]

Ana Ci Gaba Da Maida HKI Saniyar Ware A Kasashen Duniya Da Dama

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa kasashen duniya suna ci gaba da maida hKI saniyar ware, daga ciki kasar Armenia ta amince da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta wacce kuma take da birnin Kudus a matsayin babban birninta. Kafin haka dai kasashen Turai, wadanda suka hada da Island, Norwar […]

Gwamnatin Kasar Canada Ta Haramta Zaben Shugaban Kasan Iran A Kasar

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran ya bada sanarwan ceba Iraniwa mazauna kasashen Canada da Saudia ba zasu kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a gobe jumm’a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ahmad Vahidi yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa a […]

Iran: Zuba Jari Daga Kasashen Waje Ya Ninka Sau Biyu Na Zamanin Yarjeniyar JCPOA

Ministan kudi na kasar Iran ya bayyana cewa zuba jari daga kasashen a cikin shekaru uku na gwamnatin shugaba Shahid Ibrahim Ra’isi ya ninninka hatta na zamanin da yarjeniyar JCPOA take aiki a kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ehsan Khandouzi ministan kudi na kasar Iran yana fadar haka, ya kuma […]

Sojojin Yemen Sun Fidda Hotunan Hare-hare kan Jirgin Kasuwanci Na HKI

Sojojin Yemen Sun Fidda Hotunan Hare Haren Sa Suka Kai Kan Wani Jirgin ruwan kasuwanci na HKI Tare Da Amfani Da Makami Mai Linzami ‘Hypersonic” Sojojin kasar Yemen sun fidda hotunan bidiyo na hare haren da suka kaiwa wani jirgin kasuwanci na HKI a tekun Arbian, wani lokaci a bayan. Tashar talabijan ta Almasirah ta […]

Mokhber : Yarjejeniyar Iskar Gas Ta Tsakanin Iran Da Rasha Za Ta Amfani Yankin

Shugaban riko na kasar Iran Mohammad Mokhber ya ce yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tun da farko tsakanin kasar da Rasha kan yiwuwar shigo da iskar gas na Rasha zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata amfani muradun daukacin yankin. Mohammad Mokhber ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da shugaban kasar Rasha Vladimir […]

Iran Ta Yi Tir Da Harin Ta’addancin Da Ya Yi Ajalin Sojoji A Nijar

Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da ya yi ajalin sojoji da raunata wasu a Jamhuriyar Nijar. Da yake sanar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani, ya yi tir da harin, da ya yi sanadin rayuwar sojoji da kuma farar hula da raunata wasu a Nijar. Mista Kanani, ya bayyana alhininsa da […]

Iran : Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi, Ya Janye Daga Takarar Zabe

Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi daya daga cikin ‘yan takara shida da ke neman zama shugaban kasar Iran ya fice daga takarar. Hashemi, wanda tsohon dan majalisa ne kuma mataimakin shugaban kasa, ya bayyana janyewarsa daga takarar a wata sanarwa a ranar Laraba. Ya bayyana dalilin shigarsa takarar a matsayin kare tafarkin tsohon shugaban kasar Ebrahim Raeisi, […]

Ministan Tsaron Isra’ila Ya Yi Barazanar Mayar Da Lebanon Zuwa “Zamanin Dutse”

Ministan tsaron Isra’ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa “Zamanin Dutse” Ministan a wata ziyara da ya kai birnin Washington ya bayyana cewa sojojin Isra’ila suna da ikon mayar da kasar Lebanon “komawa zamanin dutse” a duk wani yaki da za ta yi da kungiyar Hizbullah, amma ya dage cewa gwamnatinsa ta fi […]

Shugaban Kenya Ya Janye Kudirin Karin Haraji, Saboda Bore A Kasar

Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya ya janye kudirin Karin haraji da ya janyo mummunar zanga zanga a kasar. Matakin shugaban kasar na zuwa ne  bayan masu zanga-zanga suka cinna wa majalisar dokokin kasar wuta ranar Talata. Cikin wani jawabi da ya yi wa kasar, ya ce ya fahimci cewa al’ummar kasar ba sa goyon […]