Iraki: Dakaru Masu Gwagwarmaya Zasu Fafatawa Da HKI Har Zuwa A Kan Iyakokin Kasar

Wani jami’in gwamnatin kasar Iraki ya bayyana cewa, idan gwamnatin HKI ta kuskura ta farwa kasar Leabanon da yaki nag aba daya, dakarun kawancen masu

Wani jami’in gwamnatin kasar Iraki ya bayyana cewa, idan gwamnatin HKI ta kuskura ta farwa kasar Leabanon da yaki nag aba daya, dakarun kawancen masu gwagwarmaya zasu fafata da su a kan iyakokin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abu Alaa Al-walae babban sakatarin rundunar Sayyidushuhadaa na kasar Iraki yana fadar haka.

Dakarun dai suna daga cikin gamayyar dakarun masu fada da ayyukan ta’addanci a kasar Iraki, ta Hashdushaabi, kuma yana daga cikin dakarun gamayyar masu gwagwarmaya a yanking aba daya.

Dakarun Sayyidushuhadaa dai ta fara kai harehare kan HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata kan HKI saboda kisan kiyashin da sojojin ta suke yi a gaza.

Ya zuwa yanzu dai dakaru masu gwagwarmaya a kasar Iraki sukan kai hare hare kan wurare masu muhimmanci a HKI daga nisan kilomita 800.

Alwalae ya kara da  cewa dakarun zasu dauke wannan tazarar idan har ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da yaki gama gari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments