Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sare’i ya bayyana cewa: Jiragen ruwan da suke kai tallafi ga yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da fuskantar hare-hare a tekun Bahar Maliya, inda a cikin sa’o’i 72 da suka gabata, sojojin Yemen suka kaddamar da hare-hare a mashigin tekun Aden, kan wasu jiragen ruwa da suka keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye, inda hare-haren suka yi sanadin nutsewarsu.
Janar Sare’i ya kara da cewa: Jirgin ruwan Verbena da suka kai masa hari ya nutse ne a mashigar Ruwan tekun Aden, bayan da ya fuskanci hare-hare da makamai masu linzami, kuma jirgin Ruwan TUTOR ya fuskanci hare-hare ne da jiragen saman yaki marasa matuki ciki da wasu makamai masu linzami, inda a halin yanzu haka jirgin yake cikin hatsarin nutsewa a tekun Aden.
Ya ci gaba da cewa: Wadannan ayyuka ne da sojojin Yemen suke gudanarwa a matsayin sadaukarwa ga ‘yan uwansu Mujahidan Gaza domin jajircewarsu a fagen jihadi, kuma hare-haren kan jiragen makiya yana zuwa ne a matsayin goron sallah ga al’ummar Falasdinu tare da fatan Allah Ya kara kiyaye su, albarkacin wannan rana ta Idin Lahiya mai albarka.