Jagoran Juyi: Yi Wa ‘Yan Sahayoniya Bara’a Wajibi Ne Ya Cigaba Bayan Aikin Haji

A cikin sakon da jagoran juyin musulunci na Iran ya aike wa da mahajjata da kuma al’ummar musulmin duniya, ya yi kira da yin bara’a

A cikin sakon da jagoran juyin musulunci na Iran ya aike wa da mahajjata da kuma al’ummar musulmin duniya, ya yi kira da yin bara’a ga ‘yan sahayoniya,tare da cewa ya zama wajibi a cigaba da aiki da shi har zuwa bayan aikin Haji.

Jagoran ya bude sakon nashi da yin godiya ga Allah tare da bayyana cewa a shekarar bana kiran da Annabi Ibrahim ya yi mutane na yin aikin haji, ya zama karba wannan sakon na tauhidi wanda yake nuni da karfin Imani da musulmi suke da shi a gaban abokan gaba.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma ce, yin dubi cikin nutsuwa da dogon tunani akan taron aikin Haji, yana bai wa musulmi karfin gwiwa da nutsuwa, haka nan kuma yana sanya tsoro a cikin zukatan musulmi.

Har ila yau Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce, wadannan dalilan ne suke sa makiya yin abinda za su iya yi, domin ganin sun bata aikin Haji da sanya shakku a cikinsa da kuma hada musulmi fada da junansu bisa sabani na mazhaba.

Da yake Magana akan sakon “Bara’a’ wanda yake kunshe a cikin aikin Haji,jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce a bana ta fi bayyana karfi bisa la’akari da manyan laifukan da ‘yan sahayoniya suke tafkawa a Gaza,wanda ba shi da tamka a wannan zamanin namu,don haka ya zama wajibi wannan bara’ar ta cigaba hatta bayan aikin Haji.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce, nuna bara’a ga ‘yan sahayoniya da masu goya musu baya, musamman Amurka, ya zama wajibi ta fito a aikace a tsakanin gwamnatoci da al’ummun muulmi domin takurwa wadannan azzaluman biyu.

A karshe jagoran juyin musuluncin na Iran, ya yi wa mahajjata addu’ar yin aikin haji karbabbe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments